Kwamitin mutum 10 da gwamnatin tarayya ta kafa domin binciken mutuwar mutane 37 da suka rasu a hannun Hukumar Tsaron Fararen Hula ta Najeriya, NSCDC, a Minna ta Jihar Neja, ya isa jihar domin fara gudanar da bincikensa.
Shugaban kwamitin, Mr Jonathan Kure, tsohon Mataimakin Darakta-Janar na Hukumar DSS mai ritaya, ya bayyana cewa kwamitin zai gudanar da aikinsa cikin ’yanci tare da neman gano ainihin abin da ya faru. Ya ce sakamakon binciken zai taimaka wajen kawo sauƙi ga waɗanda abin ya shafa da iyalansu.
Kure ya bayyana hakan ne lokacin da ya jagoranci sauran mambobin kwamitin ziyarar Gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago, a gidan gwamnati da ke Minna. Ya ce sun je jihar ne domin aiwatar da aikin da gwamnatin tarayya ta ɗora musu.
- Sultan ya yi kira ga ’yan siyasa su guji kalaman da za su jawo rikici a tsakaninsu
- Sanata Binos Yaroe ya ƙaddamar da asibitin tafi-da-gidanka a Adamawa
- Najeriya a shekaru 66: Wane ci gaba aka samu a fannin ilimi?
Shugaban kwamitin ya ce tawagar likitocin da ke cikin kwamitin ta fara aiki tun bayan ƙaddamar da kwamitin, domin tattara muhimman bayanan lafiya da na binciken kimiyya da za su taimaka wajen gano musabbabin mutuwar waɗanda suka rasu.
Ya tabbatar da cewa kwamitin zai yi amfani da ’yancin da aka ba shi wajen neman gaskiya da tabbatar da adalci, tare da gano abin da ya faru da kuma tantance alhakin duk wanda bincike ya nuna yana da hannu. Ya kuma ce duk wanda bincike ya nuna ba shi da alaƙa da abin da ya faru ba za a ɗora masa laifi ba.
Mutuwar mutanen 37 ta faru ne bayan an kama wasu da ake zargi da aikin hakar ma’adinan zinare ba bisa ka’ida ba a Minna.
Gwamnatin tarayya ta ce har yanzu ba a tabbatar da musabbabin mutuwar a hukumance ba, kuma kwamitin na da alhakin binciken yanayin kama da tsare su, tare da gano dalilin da yadda mutuwar ta faru.
A nasa bangaren, Gwamna Umaru Bago ya gode wa kwamitin bisa ziyarar, tare da tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ba shi cikakken haɗin kai da goyon bayan da ake bukata domin gudanar da binciken cikin nasara.
Gwamnan ya ce yana da yakinin cewa mambobin kwamitin, waɗanda suka fito daga fannoni daban-daban, za su gudanar da aikin cikin adalci tare da gano abubuwan da suka kai ga mutuwar mutanen.
Gwamnatin tarayya ta bai wa kwamitin makonni biyu domin kammala aikinsa da gabatar da rahoto.