Gwamnatin Tarayya ta ayyana Alhamis, 1 ga Oktoba, 2026, a matsayin ranar hutu domin bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan a madadin Gwamnatin Tarayya, inda ya taya ’yan Najeriya da ke cikin gida da ƙasashen waje murnar zagayowar ranar samun ’yancin kan ƙasar.
Ministan ya ce zaman lafiya da kwanciyar hankali na daga cikin muhimman abubuwan da ake buƙata domin ci gaban ƙasa, yana mai kira ga ’yan Najeriya da su yi koyi da kishin ƙasa da haɗin kan waɗanda suka kafa Najeriya.
Ya kuma bayyana bambancin al’adu, da harsuna da addinai a matsayin ƙarfin Najeriya, tare da jaddada cewa haɗin kai da ƙudurin ’yan ƙasa ne ginshiƙan gina ƙasa mai ƙarfi da wadata.
- Tinubu ya dawo Najeriya bayan kwana 30 baya ƙasar
- Zaman lafiya da tsaro: Nauyin kowane ɗan ƙasa ne — Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau
Tunji-Ojo ya buƙaci ’yan Najeriya da su yi amfani da bikin ’yancin kan wajen nuna kishin ƙasa, da zaman lafiya, da mutunta juna da kyautata zaman tare.
Ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da ƙarfafa tsaron ƙasa da inganta lafiyar jama’a, tare da samar da yanayin da zai bai wa ’yan Najeriya damar rayuwa, da aiki da kuma neman abin dogaro cikin kwanciyar hankali.
Gwamnatin ta ce bikin cikar Najeriya shekaru 66 ya zama wata dama ta sake tunawa da sadaukarwar jaruman da suka yi fafutukar ganin ƙasar ta samu ’yancin kai, tare da sabunta ƙudirin gina Najeriya da al’ummomi masu zuwa za su yi alfahari da ita.