Kwamishinan ’Yan Sandan Abuja, CP Ahmed Muhammed Sanusi, kwamishinan ya gargaɗi masu aikata laifuka da waɗanda ke shirin amfani da lokacin bikin wajen aikata laifi da su bar Abuja ko kuma su dakatar da duk wani aiki da ya saɓa wa doka.
Ya ce rundunar ’yan sandan FCT ba za ta bari Babban Birnin Tarayya ya zama filin aikata laifuka ba, inda ta tanadi jami’ai da dama, sintiri da sauran matakan tsaro domin tabbatar da zaman lafiya a lokacin bikin.
- An gargadi ’yan jarida kan ƙabilanci, kalaman ƙiyayya da yaɗa bayanan bogi da AI ke samarwa
- Sabuwar Najeriya mai inganci mai yiwuwa ce – Kwankwaso
Kwamishinan ya taya mazauna Babban Birnin Tarayya murnar bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai, tare da tabbatar da cewa an ɗauki matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
CP Sanusi ya buƙaci mazauna Abuja da su yi amfani da bikin domin tunawa da muhimmancin haɗin kai, zaman lafiya, kishin ƙasa da kuma ɗaukar nauyin da ke rataya a kan kowane ɗan ƙasa.
Rundunar ta kuma buƙaci mazauna Abuja su kasance cikin taka-tsantsan tare da bayar da rahoton duk wani abu da suke zargi ga jami’an tsaro.