Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta buɗe shafinta na yanar gizo na neman ma’aikatan wucin gadi da za su gudanar da ayyukan zaɓe a babban zaɓen 2027.
Hukumar ta ce shafin INECPRES ya fara karɓar aikace-aikace tun ranar 18 ga Satumba 2026, kuma za a ci gaba da karɓar aikace-aikacen har zuwa ƙarfe 12 na dare ranar 18 ga Nuwamba 2026.
Akwai guraben ayyuka daban-daban da suka haɗa da jami’an kula da masu gudanar da zaɓe, da jami’an zaɓe masu jagorantar rumfunan zaɓe, da mataimakansu, da manajojin cibiyoyin tattara ma’aikatan zaɓe da kuma ma’aikatan tallafin fasahar sadarwa.
- ’Yan sanda sun gargaɗi masu aikata laifi su bar Abuja
- Kwanaki 100 na farko sun fi mayar da hankali kan lafiya, ruwa da hanyoyin karkara – Kwali
- Rundunar sojin Najeriya ta inganta makarantun rundunar a fadin Nigeria
A cewar INEC, cancantar neman kowane matsayi tana dogara ne da matsayin mai nema, da matakin karatunsa, da wurin aiki da sauran sharuɗɗan da hukumar ta gindaya.
Wasu daga cikin waɗanda za su iya cancanta sun haɗa da masu yi wa ƙasa hidima, da tsoffin ’yan bautar ƙasa da suka cika sharuddan da aka tanada, da ɗaliban manyan makarantu da wasu ma’aikatan gwamnati.
Hukumar ta kuma jaddada cewa masu neman aikin dole ne su kasance ba ’yan wata jam’iyyar siyasa ba, sannan kada su kasance sun nuna goyon baya ga wata jam’iyya ko ɗan takara.
Haka kuma, masu nema dole ne su cika sauran sharuɗɗan da suka shafi matsayinsu kafin su fara aikace-aikacen.
Masu sha’awar neman aikin za su iya shiga shafin INECPRES ta shafin hukuma na INEC ko kuma kai tsaye ta shafin yanar gizon INECPRES.
Hukumar ta buƙaci masu nema da su karanta sharuɗɗan cancanta, su zaɓi matsayin da suka cancanta, sannan su shigar da bayanansu daidai kafin aika aikace-aikacen.
A halin yanzu, shafin INECPRES yana aiki kuma yana ci gaba da karɓar aikace-aikacen ma’aikatan zaɓen 2027.