Shugaban Ƙaramar Hukumar Kwali da ke Abuja, Daniel Nuhu Kwali, ya ce gwamnatinsa ta mayar da hankali kan ayyukan da suka shafi rayuwar al’umma kai tsaye cikin kwanaki 100 na farko na mulkinsa.

Da yake jawabi yayin bikin kwanaki 100 na mulkinsa da kuma cika shekaru 30 da kafa Kwali Area Council, shugaban ya ce abin da ya fi muhimmanci ba yawan ayyukan da aka kaddamar ba ne, illa yadda suke taimaka wa manoma, da ’yan kasuwa, da marasa lafiya da sauran mazauna yankin.

Daga cikin ayyukan da ya bayyana akwai gyaran cibiyoyin lafiya a Lambata da Kilankwa II, da gyaran makarantar firamare a Wako da kuma ayyukan inganta wasu hanyoyin karkara, ciki har da hanyar Piri-Gumbo da Dabi-Bako.

Ya kuma ce an fara samar da rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana a wasu al’ummomi domin inganta samun ruwa.

A fannin noma, gwamnatin ta ce tana kokarin tallafa wa manoma da muhimman kayan noma domin kara yawan amfanin gona da inganta rayuwar iyalan da suka dogara da noma.

Wannan na zuwa ne a wani yanki da noma ke daga cikin muhimman hanyoyin samun abin dogaro ga al’umma.

Bikin na kwanaki 100 ya kuma kasance wata dama ga gwamnatin ta nuna wasu shirye-shiryen tallafa wa al’umma, inda aka raba babura 30 ga jami’an tsaro da wasu masu cin gajiyar shirin, injinan dinki 60, injinan nika da kuma kwalayen maganin ciyawa 130 ga manoma.

An kuma bayar da littattafan rubutu 40,000 ga makarantun firamare na LEA a Kwali.

Sai dai shugaban ya amince cewa kwanaki 100 ba su isa a auna cikakken aikin gwamnati ba, inda ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da sauraron bukatun al’umma, da tuntubar masu ruwa da tsaki da kuma amfani da albarkatun da aka damƙa mata wajen magance matsalolin da suka fi shafar jama’a.

A nasa bangaren, Etsu Kwali kuma shugaban Majalisar Sarakunan Kwali, Luka Nizassan III, ya yi kira ga mazauna yankin da su ci gaba da zaman lafiya tare da bai wa gwamnati goyon baya wajen gudanar da shirye-shiryenta.

Ƙaramar hukumar Kwali na daga cikin yankunan gudanarwa shida na Abuja, kuma an kafa ta ne a ranar 1 ga Oktoba, 1996.

A yayin bikin cika shekaru 30 da kafuwarta, an jaddada bukatar ci gaba da hada kai tsakanin gwamnati, sarakunan gargajiya da al’umma domin bunkasa ayyukan da suka shafi rayuwar jama’a kai tsaye.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *