Kamfanin Dangote (DIL), daya daga cikin masu daukar nauyin Baje Kolin Kasuwanci na Abuja karo na 21, zai gabatar da shirin sayar da hannun jarin matatar Dangote da masana’antar sinadaran man fetur, wato IPO, a yayin bikin musamman na kamfanin.

 

Za gudanar da bikin Dangote Special Day ne a ranar Juma’a 2 ga Oktoba, inda za a gudanar da tattaunawa tsakanin manyan jami’an kamfanin, gwamnati, ‘yan kasuwa da wakilan kamfanoni masu zaman kansu kan rawar da matatar Dangote ke takawa wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya.

 

Kamfanin ya ce taron zai bai wa masu son zuba jari, ‘yan kasuwa da sauran mahalarta damar tattaunawa kai tsaye da wakilan Dangote tare da samun karin bayani kan shirin sayar da hannun jarin matatar da kuma muhimmancinsa ga tattalin arzikin kasar.

 

Taken taron shi ne “Dangote Refinery, Vision 2030, inda za a tattauna gudunmawar matatar wajen samar da wadatar makamashi, da bunkasa masana’antu, da kasuwanci, da samar da ayyukan yi, da tara haraji da habaka tattalin arzikin Najeriya.

 

Za kuma a mayar da hankali kan yadda karuwar tace man fetur a cikin gida za ta iya rage dogaro da shigo da man fetur daga kasashen waje, da rage fitar da kudaden kasashen waje, tare da karfafa masana’antun cikin gida da samar da sabbin damarmaki ga harkokin kasuwanci.

 

Shirin IPO zai kasance daya daga cikin muhimman batutuwan taron, inda mahalarta za su tattauna yadda sayar da hannun jarin zai kara damar jama’a da masu zuba jari shiga mallakar daya daga cikin manyan kadarorin masana’antu a Afirka, tare da bunkasa kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya.

 

Bayan tattaunawar, masu ziyartar baje kolin za su samu damar ganin rumfar Dangote, inda kamfanin zai baje kolin kayayyaki da ayyukansa da suka hada da siminti, da sukari, da gishiri da kayan dandano, da marufi da sauran bangarorin kasuwancinsa.

 

Baje kolin kasuwancin na Abuja, wanda Abuja Chamber of Commerce and Industry (ACCI) ta shirya, ana sa ran zai hada daruruwan kamfanoni, da ‘yan kasuwa, da masu zuba jari, da masu tsara manufofi da jama’a. Dangote ya ce halartarsa da daukar nauyin taron na nuna goyon bayansa ga harkokin kasuwanci, da zuba jari, da samar da ayyukan yi da hadin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *