Rundunar Sojin Najeriya ta ce tana ci gaba da inganta tsarin iliminta ta hanyar gyaran gine-gine, da samar da kayan koyarwa da inganta yanayin karatu a makarantun rundunar da ke sassa daban-daban na ƙasar.
Mukaddashin Kwamandan Ilimi na Rundunar Sojin Najeriya, Birgediya Janar Yusha’u Dogara Ahmed, ya bayyana haka yayin wata ziyarar tantancewa da ya kai makarantun Command Secondary School da ke Makurdi a Jihar Benue, da kuma makarantun rundunar da ke Faskari da Barkiya a Jihar Katsina.
A Makurdi, tawagar ta duba azuzuwa, da dakunan kwanan ɗalibai, da ɗakin cin abinci, da ɗakin karatu da sauran ayyukan da aka aiwatar a ƙarƙashin shirin shiga tsakani na Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu.
- Kwanaki 100 na farko sun fi mayar da hankali kan lafiya, ruwa da hanyoyin karkara – Kwali
- Dangote ya dauki nauyin baje kolin kasuwanci a Abuja
- ’Yan sanda sun gargaɗi masu aikata laifi su bar Abuja
Rundunar ta ce ayyukan sun taimaka wajen inganta abubuwan more rayuwa da yanayin karatu a makarantar, yayin da aka buƙaci mahukuntan makarantun su tabbatar da kula da kayan aikin da aka samar tare da amfani da su yadda ya kamata.
Ziyarar ta kuma shafi makarantun Command Secondary School Boys Faskari da Command Secondary School Girls Barkiya a Katsina, inda aka duba yanayin koyarwa, gudanarwa da abubuwan more rayuwa tare da gano wasu bukatun da ke buƙatar ƙarin kulawa.
Rundunar ta ce sakamakon tantancewar zai taimaka wajen tsara ƙarin matakan inganta makarantun, da tabbatar da cewa jarin da ake zubawa a fannin ilimi ya haifar da ingantaccen koyarwa, koyo da ɗabi’a ga ɗalibai.