Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yaba wa Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa da Laifukan Tattalin Arziki ta Ƙasa (EFCC) kan yadda take yaƙi da laifukan kuɗi da cin hanci da rashawa, yana mai cewa ayyukan hukumar sun tabbatar da amincewar da gwamnati ta yi mata.
Tinubu ya bayyana hakan ne ranar Juma’a, 2 ga Oktoba, 2026, yayin ƙaddamar da sabon ofishin hukumar na shiyyar Awka, babban birnin Jihar Anambra.
Da yake samun wakilcin Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, a wajen taron, Shugaban Ƙasar ya ce nasarorin EFCC ya bayyana ne ta hanyar yawan hukuncin da kotuna suka yanke, da dawo da kadarori da kuɗaɗen da ake zargin an samu ta haramtacciyar hanya, da kuma wasu matakan da hukumar ta ɗauka wajen yaƙi da cin hanci.
- Rundunar sojin Najeriya ta inganta makarantun rundunar a fadin Nigeria
- Kwanaki 100 na farko sun fi mayar da hankali kan lafiya, ruwa da hanyoyin karkara – Kwali
A nasa jawabin, Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya ce tsakanin Oktoba 2023 zuwa Yuli 2026, hukumar ta karɓi koke-koke 49,673, ta gudanar da bincike kan shari’u 39,615, sannan ta gurfanar da mutane a kan shari’u 14,476.
Ya ce an samu hukunci a shari’u 10,872, abin da ya ba hukumar kaso 75.1 cikin 100 na nasarar hukuncin da aka yanke idan aka kwatanta da yawan shari’un da ta shigar.
Olukoyede ya kuma bayyana cewa a cikin wannan lokaci, hukumar ta kwato sama da Naira tiriliyan 1.23, da dala miliyan 684.47, baya ga wasu kuɗaɗen kasashen waje. Ya ce a farkon rabin shekarar 2026 kaɗai, hukumar ta samu nasara a hukunci 1,370 daga cikin shari’u 1,889 da ta shigar.
Ya ce sabon ofishin na Awka ba wai kawai an buɗe shi ne domin faɗaɗa ayyukan EFCC ba, amma kuma domin kusantar da hukumar ga jama’a da cibiyoyin tattalin arziki na Anambra da Imo.
Olukoyede ya ce hukumar za ta ƙara mayar da hankali kan rigakafin cin hanci ta hanyar aiki da hukumomin gwamnati, ’yan kasuwa, cibiyoyin kuɗi, makarantu, ƙungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki.
Ya kuma bayyana cewa hukumar za ta ci gaba da amfani da hanyoyin zamani wajen karɓar bayanai daga jama’a kan ayyukan da ake zargi da saba wa doka, yana mai jaddada cewa masu tona asirin cin hanci su gabatar da sahihan bayanai, ba tare da amfani da rahoton ƙarya wajen ɗaukar fansa ko sasanta husuma ba.
Gwamnonin Anambra da Imo, Chukwuma Soludo da Hope Uzodinma, sun halarci ƙaddamarwar tare da wasu manyan jami’an gwamnati da ’yan majalisa, inda suka bayyana goyon bayansu ga ayyukan hukumar.