Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Rotimi Amaechi, ya kalubalanci Shugaba Bola Tinubu da ya sauke farashin man fetur zuwa naira 600 kan kowace lita.

Amaechi ya ce idan farashin man fetur ya sauka zuwa wannan adadi, zai janye daga tikitin ADC tare da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, sannan ya yi wa Shugaba Tinubu kamfen a zaɓen 2027.

Amaechi ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan jawabin Tinubu na ranar samun ’yancin kan Najeriya da kuma ikirarin shugaban ƙasar cewa Najeriya ta shiga wani “zamanin wadata”, a wata hira da shirin Politics Today na Channels Television ranar Juma’a.

Amaechi ya nuna shakku kan wannan ikirari, yana mai cewa ya kamata ’yan Najeriya su duba ko sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnati ta aiwatar sun haifar da raguwar farashin kayayyaki da inganta rayuwar jama’a.

Ya yi amfani da farashin man fetur a matsayin ma’aunin tantance ikirarin gwamnati kan tattalin arziki, inda ya ce shi da kansa zai je gidan mai domin tabbatar da ko farashin ya sauka zuwa naira 600 kan kowace lita.

Amaechi ya ce duk wanda yake shakkar alkawarin da ya yi zai iya zuwa da kyamara tare da shi, inda zai je gidan mai ya sayi man fetur da kansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *