Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ya rantsar da sabbin manyan sakatarorin 20 domin ƙarfafa aikin gwamnati da inganta ayyukan ma’aikatan jihar.
Gwamnan ya ce naɗin ba wai kawai wata alama ce ta amincewa da ƙwarewa da sadaukarwar jami’an ba, illa ƙarin nauyin da aka ɗora musu na yi wa jihar hidima yadda ya kamata.
- ’Yan sanda sun dakile harin ’yan bindiga a Sokoto, sun kwato makaman roka
- Abdul Samad Rabiu ya ziyarci Tinubu, ya taya Najeriya murnar cika shekaru 66
Uzodimma ya buƙaci sabbin Sakatarorin su gudanar da ayyukansu bisa kishin ƙasa, da ƙwarewa, gaskiya da riƙon amana, tare da tabbatar da inganci da tasiri a aikin gwamnati.
A ranar 22 ga Satumba, gwamnatin jihar ta sanar da amincewa da naɗin manyan sakatarorin 20, inda ta ce za su nuna ƙwarewarsu wajen gudanar da ayyukan da aka ɗora musu.