Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sakkwato ta ce ta dakile wani harin da wasu ’yan bindiga suka kai kauyen Tsabre da ke ƙaramar hukumar Isa, inda ta kwato makaman roka guda biyu da wasu kayayyaki da maharan suka bari suka tsere.
A cewar rundunar, maharan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 1:00 na dare, inda suka rika harbe-harbe domin tayar da hankalin mazauna yankin. Bayan samun kiran neman agaji, jami’an ’yan sanda daga Isa tare da rundunar yaƙi da masu garkuwa da mutane da sauran jami’an tsaro sun isa wurin, inda aka yi musayar wuta da maharan.
- Tinubu ya yaba wa EFCC, ya ce ta tabbatar da amincewar da aka yi mata
- ’Yan sanda sun dakile harin ’yan bindiga a Sokoto, sun kwato makaman roka
Rundunar ta ce jami’anta sun yi nasarar tilasta wa ’yan bindigar tserewa zuwa dajin da ke kusa, inda daga bisani aka gudanar da bincike a cikin dazuzzukan.
Daga cikin abubuwan da aka kwato akwai makaman roka guda biyu, harsasai guda biyu na bindigar AK-47, wayar Tecno, fitilar hannu, hular sojan Najeriya, hulunan sanyi, takalma guda biyar da rigar kariya daga ruwa.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Sakkwato, Hayatu Hassan Shaffa, ya jaddada cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Ya kuma bukaci jama’a su kasance cikin taka-tsantsan tare da kai rahoton mutanen da ake zargin sun samu raunin harbin bindiga ga ’yan sanda.