Emmanuel Okibe Ogbonna, dan wasan tsalle na Najeriya

Ɗan wasan tsalle na masu Buƙata ta musamman na Najeriya, Emmanuel Okibe Ogbonna, ya lashe lambar azurfa a gasar tsalle mai tazara ta maza rukunin T47 a Gasar masu Buƙata ta musamman ta ƙasa da ƙasa da aka yi a Krasnodar, da ke Rasha.

Ogbonna ya yi tsalle mafi tsayi na mita 6.28 don kammala gasar a matsayi na biyu a cikin fafatawa mai zafi, yayin da zakaran gasar ɗan ƙasar Rasha ya lashe zinare bayan ya yi tsallen mita 6.48.

Wannan nasara ta baiwa Ogbonna danar samun tikitin shiga Gasar masu Buƙata ta musamman ta Duniya ta 2027 da za a yi a Tashkent, da ke Uzbekistan.

Hakan ya ƙarawa ɗan wasan wata daraja da kuma alfahari a rayuwarsa ta wasanni a duniya.

Shugaban Kwamitin wasan masu bukata ta musamman na Najeriya (NPC Nigeria), Sunday Odebode, ya taya Ogbonna murna kan wannan ƙwazon kuma ya bayyana sakamakon a matsayin ci gaba mai ƙarfafa gwiwa ga wasannin masu Buƙata ta musamman na Najeriya.

Lambar azurfa da Ogbonna ya samu a Krasnodar ta ba Najeriya kyakkyawan sakamako a fagen wasannin masu buƙata ta musamman na duniya kuma ta bai wa ɗan wasan damar samun tikitin shiga gasar duniya ta 2027 a Uzbekistan tun da wuri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *