An sanya Najeriya a Rukuni na A a gasar farko ta Cin Kofin Duniya na ‘yan ƙasa da shekaru 15 na 2026, wanda aka shirya gudanarwa a ƙasar Azerbaijan daga 24 zuwa 30 ga Oktoba.
Tawagar matasan Super Eagles za ta fafata da Cyprus, da Gambia, da Jordan, da Pakistan da Sudan ta Kudu a matakin rukuni na gasar.
-
Kocin tawagar Kwallon rairayi ta Najeriya ya yabawa Hukumar NFF kan wasan Gwaji da Senegal
-
Najeriya ta samu tikitin shiga Gasar masu buƙata ta musamman ta Duniya ta 2027
-
Gasar Olympics ta 2028: Eguavoen ya gayyaci Ajibade da wasu ‘yan wasa 27
Gasar ta zo da sabon tsarin wasa na mutum 8 daga kowace tawaga a cikin fili, inda hakan zai haɗa kan matasan tawagu daga sassa daban-daban na duniya don bikin kwallon kafa na tsawon mako guda.
Taron zai ƙunshi kwanaki shida na wasanni, inda ake sa ran za a buga wasanni kusan 950.
An shirya gudanar da gasar Cin Kofin Duniyar da kuma Bikin na yan kasa da shekaru 15 daga 24 zuwa 30 ga Oktoba, 2026, a Azerbaijan.