Gwamnatin Tarayya ta ce tana sa ran samar da kusan guraben ayyuka 10,000 daga kowanne babban mayanka da zai iya sarrafa shanu 500 a rana, idan aka kafa shi ta hanyar haɗin gwiwar gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.
Ministan harkokin Kiwo, Idi Maiha, ne ya bayyana haka yayin wata ziyarar aiki da ya kai wa Gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago, a Minna, inda ya ce shirin na daga cikin matakan da ake ɗauka domin sauya tsarin kiwon dabbobi daga jigilar dabbobi masu rai zuwa sarrafa nama a cikin gida.
Mista Maiha ya ce manyan mayankan za su samar da damammaki ga matasa a fannoni da suka haɗa da kiwon shanu, noman ciyawa da abincin dabbobi, ayyukan kiwon lafiya na dabbobi, sufuri, sarrafa nama da ajiyarsa a cikin sanyi.
- Mutane 20 sun mutu a hatsarin mota a Plateau
- Najeriya za ta kara a rukunin A na Gasar Cin Kofin Duniya
Ya ce Najeriya na fuskantar asarar nauyin dabbobi da sauran matsaloli sakamakon jigilar shanu daga Arewa zuwa Kudu, yana mai cewa ya kamata a koma tsarin jigilar naman da aka sarrafa cikin tsaftataccen yanayi maimakon jigilar dabbobi masu rai.
Ministan ya kuma bayyana abinci da ciyawar dabbobi, da inganta nau’in dabbobi da kula da lafiyarsu a matsayin manyan abubuwan da ma’aikatarsa ta mayar da hankali a kai.
A cewarsa, inganta kiwo zai taimaka wajen ƙara samar da madara tare da rage dogaro da kayayyakin madara da ake shigowa da su daga ƙasashen waje.
A nasa bangaren, Gwamna Umaru Bago ya ce Jihar Neja na shirin ƙara noman abincin dabbobi domin magance ƙarancin wuraren kiwo.
Ya kuma ce wani shirin da ake aiwatarwa tare da tallafin Bankin Fitar da Kayayyaki na Saudiyya zai samar da ruwa, abinci, wuraren kiwo da ayyukan kula da lafiyar dabbobi.
Bago ya kuma ce akwai wani tsari da zai bai wa Jihar Neja damar samar da shanu kusan 200 a kullum zuwa wata masana’antar sarrafa abinci a Abuja, inda ake sa ran tsarin zai samar da kusan guraben ayyuka 20,000 kai tsaye da a kaikaice.
Gwamnatin Tarayya ta ce manufar ita ce a gina tsarin kiwo da sarrafa dabbobi mai haɗa manoma, masu kiwo, masu sarrafa nama, masu samar da abinci da ciyawa, likitocin dabbobi da masu sufuri, domin ƙara darajar kayayyakin kiwo da samar da ayyukan yi a cikin gida.