Shugabannin jam’iyyar APC a yankin Arewa ta Tsakiya sun ƙaddamar da wani sabon gangamin wayar da kan al’umma da neman goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa Kashim Shettima a zaɓen 2027.
An ƙaddamar da shirin ne a Abuja, inda Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, da Gwamnan Nasarawa Abdullahi Sule da sauran shugabannin jam’iyyar suka bayyana aniyar ƙara kai saƙon jam’iyyar zuwa matakin al’umma.
Shugabannin sun ce burinsu shi ne ganin yankin ya samar da yawan ƙuri’u ga Tinubu a zaɓen 2027.
- NAOWA ta tallafa wa malaman makarantu, da matan jami’an soja a Kaduna
- Rundunar Sojin Sama ta karɓi sabbin jirage masu saukar ungulu guda biyu
An kuma tsara gudanar da babban gangami a Lafia, jihar Nasarawa, a ranar 10 ga Oktoba, tare da shirya tarukan tuntuba da sauran ayyukan wayar da kan jama’a a yankin.
Haka kuma, an amince da kafa kwamitin sulhu domin magance wasu matsalolin cikin gida na jam’iyyar, yayin da aka shirya gudanar da shirin tallafin lafiya ga al’ummomin da ke cikin buƙata.
Arewa ta Tsakiya ta ƙunshi jihohin Benue, Kogi, Kwara, Nasarawa, Neja da Filato, da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.