’Yan sandan Babban Birnin Tarayya Abuja sun kama wani mutum bisa zargin lalata da wata yarinya ’yar shekara 12 a wani abin hawa da aka ajiye a kusa da filin motocin haya na Airport Bridge.
Rundunar ’yan sandan ta ce jami’an sashen yaƙi da garkuwa da mutane ne suka gano lamarin a ranar 2 ga Oktoba yayin da suke sintiri.
Jami’an sun ce sun lura da wata mota mai duhun gilashi tana girgiza, lamarin da ya sa suka duba cikin motar, inda suka tarar da wanda ake zargin tare da yarinyar.
- Gwamnan Kano ya nemi a ci gaba da goyon bayan Tinubu a 2027
- Ranar Dabbobi ta Duniya 2026: Ƙaruwar Matsalar Sauyin Yanayi na Jefa Dabbobi Cikin Hatsarin Ƙarewa
Binciken farko na ’yan sandan ya nuna cewa ana zargin wanda ake zargin da yin lalata da yarinyar a wurin a lokuta daban-daban, tare da yi mata barazanar cutar da ita idan ta bayyana abin da ke faruwa.
Rundunar ta ce binciken lafiya ya nuna cewa yarinyar na dauke da ciki na kimanin watanni uku, kuma a halin yanzu tana samun kulawar lafiya yayin da wanda ake zargin yake hannun ’yan sanda.
’Yan sanda sun ce za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala bincike, yayin da Kwamishinan ’Yan Sandan Abuja, CP Ahmed Muhammed Sanusi, ya yi kira ga iyaye da masu kula da yara da su kara sanya ido kan tsaro da lafiyar yaran da ke karkashinsu.