Gwamnan Jihar Taraba, Dr Agbu Kefas, ya gana da masu haƙar ma’adinai na gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki a fannin, inda ya bayyana shirin gwamnati na samar da tsarin da zai tabbatar da haƙar ma’adinai cikin aminci, bin doka da kuma kare al’umma.
A yayin taron da aka gudanar a Jalingo, gwamnan ya ce mutane da dama sun dogara da haƙar ma’adinai wajen samun abin tafiyar da rayuwa, don haka gwamnati ba ta son hana sana’ar, sai dai ta tsara ta yadda za ta kasance mai amfani tare da rage illolin da take haifarwa ga muhalli da lafiyar jama’a.
- Ranar Dabbobi ta Duniya 2026: Ƙaruwar Matsalar Sauyin Yanayi na Jefa Dabbobi Cikin Hatsarin Ƙarewa
- An kama wani mutum bisa zargin lalata da yarinya ’yar shekara 12 a Abuja
Kefas ya ce gwamnatinsa za ta samar da ƙa’idojin haƙar ma’adinai cikin ɗa’a da kula da lafiyar al’umma, ciki har da kare hanyoyin ruwa, horas da masu haƙar ma’adinai da ma’aikatan lafiya, da kuma samar da tsarin gano tare da gyara ayyukan da ke da haɗari.
A wani ɓangare, gwamnan ya bayyana cewa gwamnati ta ware Naira biliyan 2.5 domin tallafa wa gidaje masu fama da ƙalubalen rayuwa, matasa da kuma al’ummomin da rikice-rikice suka shafa.
Kudin ya haɗa da Naira miliyan 500 ga shirin TARABA CARES, da Naira biliyan ɗaya ga Hukumar Raya Matasa ta jihar, da kuma Naira biliyan ɗaya domin tallafi da farfaɗo da al’ummomin da rikici ya shafa.
Gwamnan ya umarci hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da cewa an yi amfani da kuɗaɗen yadda ya kamata, tare da bayyana bayanai kan yadda ake aiwatar da shirye-shiryen domin tabbatar da gaskiya da riƙon amana.