Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, ya yi kira da a kafa reshen Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa (EFCC) a Jihar Imo, domin sauƙaƙa wa mazauna yankin Kudu maso Gabas hulɗa da hukumar.
Uzodinma ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan buɗe sabon ofishin shiyya na EFCC a Awka, Jihar Anambra, yana mai cewa matakin zai kusantar da ayyukan hukumar ga jama’a tare da rage musu wahalar tafiya zuwa Legas ko Abuja domin gudanar da harkokin da suka shafi EFCC.
- Kefas ya bayyana sabon tsarin hakar ma’adinai a Taraba
- An kama wani mutum bisa zargin lalata da yarinya ’yar shekara 12 a Abuja
Gwamnan ya ce rarraba ofisoshin hukumar zuwa yankuna zai ƙara inganta saurin aiki, da sauƙaƙa samun damar yin hulɗa da hukumar, tare da ƙarfafa yaƙi da laifukan da suka shafi kuɗi da tattalin arziki.
Ya ƙara da cewa kafa reshe a Imo zai taimaka wajen faɗaɗa ayyukan hukumar a Kudu maso Gabas, tare da tabbatar da cewa mazauna yankin sun samu damar cin moriyar ayyukan EFCC ba tare da fuskantar tsadar tafiya zuwa wasu jihohi ba.