Majalisar Koli ta Harkokin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), ƙarƙashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ta faɗaɗa tare da sake fasalin Majalisar Zartarwarta ta Ƙasa.
An cimma matsayar ne a babban taron majalisar da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis, 1 ga Oktoba 2026, wanda ya samu halartar shugabannin Musulmi da manyan limaman masallatan Juma’a daga jihohin ƙasar 36 da Babban Birnin Tarayya Abuja.
Sabbin jami’an da aka naɗa sun haɗa da Farfesa Mahfouz Adedimeji a matsayin Mataimakin Babban Sakatare na Ƙasa, Farfesa Salisu Shehu a matsayin Mataimakin Babban Sakatare na Harkokin Ƙasa, yayin da Mista Abeny Mohammed (SAN) zai kasance Mataimakin Babban Sakatare na Harkokin Kamfanoni.
Haka kuma, an naɗa Dakta Bala Muhammad a matsayin Mataimakin Babban Sakatare mai kula da harkokin gudanarwa, Dakta Umar Jibrilu Gwandu a matsayin Jami’in Hulɗa da Jama’a, yayin da Hajiya Sekinat Lawal ta zama Mataimakiyar Jami’in Hulɗa da Jama’a.
Sauran waɗanda aka naɗa sun haɗa da Dakta Mairo Mandara a matsayin Jami’ar Ci Gaba, Arc Abdullahi Musa PenAbdul a matsayin Mataimakin Jami’in Ci Gaba mai kula da fasaha, da Farfesa Fatimah Abdulkarim a matsayin Jami’ar Harkokin Iyali.
Majalisar ta ce matakin faɗaɗa majalisar zartarwar na daga cikin sauye-sauyen da aka amince da su domin ƙarfafa ayyukanta da inganta tsarin gudanar da harkokin Musulmi a ƙasa.