Kungiyar Injiniyoyi ta Najeriya (NSE), reshen Warri, ta bukaci gwamnati da ta sake fasalin tare da gina cikakkiyar gada a yankin Agbarho da ke kan hanyar Gabas zuwa Yamma a Jihar Delta, bayan wani bangare na hanyar ya ruguje sakamakon ruwan sama mai karfi.
Shugabar kungiyar reshen NSE na Warri, Mrs Queen Chigbo, ta bayyana hakan yayin da tawagar injiniyoyin ta kai ziyara domin duba matsalar hanyar a karamar hukumar Ughelli ta Arewa.
A cewarta, magudanar ruwan da ke karkashin hanyar ba ta da girman da zai iya daukar yawan ruwan da ke kwarara a yankin, lamarin da ya taimaka wajen haddasa ambaliyar ruwa da rugujewar hanyar.
- Majalisar Musulunci ta Ƙasa ta faɗaɗa majalisar zartarwarta
- Uzodinma ya nemi a buɗe reshen EFCC a Imo
Ta ce maimakon a ci gaba da amfani da irin wannan magudanar ruwa, ya kamata a sake fasalin wurin tare da gina gada ta zamani da za ta iya jure yawan ruwan da ke kwarara domin kauce wa sake faruwar irin wannan matsala a nan gaba.
Rugujewar hanyar ta sanya an dakatar da zirga-zirga a bangarorin titin biyu, lamarin da ya jefa matafiya da masu ababen hawa cikin wahala. Sai dai an ce an karfafa daya daga cikin hanyoyin wucin gadi domin rage matsalar zirga-zirga.
NSE ta yabawa gwamnatin Jihar Delta da sauran masu ruwa da tsaki bisa matakan gaggawa da suka dauka, tare da jaddada bukatar a nemo mafita mai dorewa ga matsalar hanyar.
