Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, IGP Olatunji Rilwan Disu, ya gana da babban sakataren hukumar INTERPOL, Valdecy Urquiza, a hedikwatar hukumar da ke Lyon, Faransa, domin ƙarfafa haɗin gwiwar Najeriya da ƙasashen duniya wajen yaƙi da manyan laifuka.
Ziyarar ta kasance karo na farko da IGP Disu ya kai hedikwatar INTERPOL tun bayan hawansa matsayin shugaban rundunar ’yan sandan Najeriya, inda aka tattauna hanyoyin inganta musayar bayanan sirri da binciken laifukan da suka shafi ƙasashe daban-daban.
Daga cikin batutuwan da aka tattauna akwai yaƙi da laifukan yanar gizo, ta’addanci, laifukan kuɗi, ƙungiyoyin masu aikata laifuka, bin diddigin waɗanda ake nema ruwa a jallo da kuma amfani da bayanan da manhajojin INTERPOL ke samarwa.
- Babu ɗalibin Gamji College da aka sace — Gwamnatin Sokoto ta musanta rahoton Sahara Reporters
- Tinubu ya taya Dele Alake murnar cika shekaru 70
Taron ya kuma mayar da hankali kan ƙara inganta ƙarfin ’yan sandan Najeriya wajen nazarin bayanan laifuka, gudanar da bincike tsakanin ƙasashe da kuma dakile ayyukan ƙungiyoyin masu aikata laifuka da ke amfani da iyakokin ƙasashe wajen ɓoye ayyukansu.
IGP Disu ya samu rakiyar shugaban INTERPOL Nigeria da National Central Bureau Abuja, AIG Olaolu Adegbite; Daraktan cibiyar yaƙi da laifukan yanar gizo ta ’yan sandan Najeriya, AIG Ezima Akaninyene Ifem; shugaban sashen yaƙi da ta’addanci, AIG Akoh Benedict Gabriel; da CP Ojajuni Olubode, mamba a kwamitin INTERPOL na Afirka.
Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta ce za ta ci gaba da ƙarfafa haɗin gwiwa da INTERPOL da sauran hukumomin tsaro na ƙasashen duniya, musamman wajen amfani da fasaha, bayanan sirri da hanyoyin aikin ’yan sanda na duniya wajen dakile barazanar tsaro da laifukan da suka ratsa iyakokin ƙasashe.