Gwamnatin Jihar Sokoto ta musanta rahoton da ya ce an sace ɗalibai 18 na Gamji College of Health Technology da ke Sokoto, tana mai cewa babu wani ɗalibin makarantar da aka sace.
Gwamnatin ta ce rahoton da aka wallafa ba shi da tushe, inda ta bayyana cewa mutumin da aka sace a lamarin shi ne Halima Sokeni, tsohuwar ɗalibar Gamji College of Nursing Sciences da ke unguwar More da ke Sokoto.
- Tinubu ya yi alhinin mutuwar jami’an NAF a hatsarin jirgin Ondo, ya umarci a yi bincike
- Tinubu ya taya Dele Alake murnar cika shekaru 70
A cewar gwamnatin, Sokeni ta kammala karatunta a makarantar a watan Satumban 2026, inda ta samu takardar shaidar ungozoma.
Ta ce an sace ta ne a ranar Alhamis, 1 ga Oktoba, 2026, yayin da take kan hanyar komawa gida tare da wasu fasinjoji a Jihar Neja.
Gwamnatin ta bukaci jama’a da su yi watsi da rahoton da ya ce ɗalibai 18 na Gamji College ne aka sace, tana mai cewa rahoton ba daidai ba ne.
Haka kuma, ta yi kira ga ’yan jarida da kafafen yaɗa labarai da su riƙa tabbatar da sahihancin bayanai kafin wallafa su, domin kauce wa yaɗa labaran ƙarya da ka iya haifar da tsoro ko ruɗani a tsakanin jama’a.