Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana alhininsa kan hatsarin jirgin saman Nigerian Air Force, NAF, da ya rutsa da jami’an rundunar a jihar Ondo.
Jirgin ATR-42 ɗin ya yi hatsarin ne a safiyar Litinin kusa da wani sansanin sojojin ruwa da ke yankin Igbokoda, yayin da yake kan hanyar tafiya daga Benin zuwa Legas domin gudanar da aikin yau da kullum.
A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan fasinjoji 25 da ma’aikatan jirgin bakwai da lamarin ya shafa, da kuma shugabannin da jami’an rundunar sojin saman Najeriya.
- ’Yan sanda sun gayyaci Aminu Abdullahi Warkal kan zargin nuna bindiga a Kano
- Tinubu ya koma Abuja bayan kwana shida a Lagos
Shugaban ƙasar ya ce mutuwar jami’an rundunar lokaci ne mai matuƙar ciwo ga sojojin Najeriya da ƙasar baki ɗaya, yana mai cewa jami’an rundunar sojin sama na sadaukar da rayukansu wajen kare ƙasar.
Tinubu ya ce ya umarci rundunar sojin saman Najeriya da ta fara gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin hatsarin da kuma ɗaukar matakan da za su taimaka wajen hana sake faruwar irin wannan lamari.
Ya kuma yabawa rundunar NAF bisa gaggauta kunna aikin ceto da neman waɗanda hatsarin ya rutsa da su, tare da yabawa jami’an agaji na farko da gwamnatin jihar Ondo kan irin martanin da suka bayar a wurin da hatsarin ya afku.
Shugaban ƙasar ya yi addu’ar Allah Ya jiƙan jami’an da suka rasa rayukansu, tare da bai wa iyalansu da rundunar sojin saman Najeriya ƙarfin jure wannan rashi.