Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta gayyaci Hon. Aminu Abdullahi Warkal domin yi masa tambayoyi kan wani bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta, inda ake zarginsa da nuna bindiga a yayin wani taron siyasa.

Rundunar ta ce jami’anta sun gano bidiyon ne yayin gudanar da sintirin yanar gizo, inda ake ganin Warkal da wata bindiga da ake zargin Pump Action Rifle ce.

Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya umarci a gayyaci Warkal zuwa hedikwatar rundunar da ke Bompai, Kano, inda a yanzu yake a hannun sashen binciken sirri na rundunar domin gudanar da bincike.

’Yan sandan sun ce idan binciken ya tabbatar da zargin, nuna bindigar na iya zama take dokar mallakar makamai, tare da barazana ga zaman lafiya da tsaron jama’a.

Rundunar ta gargadi ’yan siyasa da magoya bayansu da su guji duk wani aiki da zai iya haddasa tashin hankali, tana mai cewa za ta dauki mataki kan duk wanda ya karya doka ba tare da la’akari da matsayinsa ba.

 

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *