Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai bar Legas zuwa Abuja ranar Talata, bayan shafe kwanaki shida a tsohuwar hedikwatar gwamnatin tarayya.
Shugaban ya isa Legas ne a ranar Talata, 29 ga Satumba, bayan kammala hutun shekara a London da Paris.
- NDC ta musanta zargin Seriake Dickson na aiki da APC
- ’Yan sanda sun gayyaci Aminu Abdullahi Warkal kan zargin nuna bindiga a Kano
A lokacin zamansa a Legas, Tinubu ya gabatar da jawabi ga ’yan Najeriya a ranar 1 ga Oktoba, yayin bikin cikar Najeriya shekaru 66 da samun ’yancin kai.
A wannan rana kuma, ya halarci bikin ƙaddamar da shirin fim ɗin MKO, wanda ke ba da labarin rayuwa da gwagwarmayar marigayi MKO Abiola da fafutukar dawo da dimokuraɗiyya bayan soke zaɓen 12 ga Yuni.
Shugaban ya kuma ziyarci Sarkin Legas, Oba Rilwan Babatunde Akiolu, a fadarsa da ke Iga Iduganran, ranar Lahadi.
Shugaba Tinubu zai koma Abuja a yau domin ci gaba da ayyukan gwamnati.