Jam’iyyar NDC ta musanta zargin cewa shugabanta na ƙasa, Sanata Seriake Dickson, na da wata yarjejeniya ta ɓoye da jam’iyyar APC mai mulki ko wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a cikinta.
A wata sanarwa da Sakataren Yada Labarain jam’iyyar na Ƙasa, Osa Director, ya fitar ranar 5 ga Oktoba, NDC ta ce zargin ba shi da tushe, tana mai bayyana shi a matsayin ƙoƙarin ɓata sunan ɗan siyasar gabanin zaɓen 2027.
Jam’iyyar ta ce Dickson, wanda ya yi shekaru sama da bakwai a Majalisar Dattawa, ya kasance mai tsayawa kan matsayinsa kan muhimman batutuwan ƙasa, tana mai cewa tarihin siyasarsa ya nuna ba shi da wata manufa ta yin aiki a ɓoye domin cutar da jam’iyyarsa.
- ’Yan Sandan FCT sun yi gargadi kan motocin da ba su da lambar rajista
- Atiku ya yi kira da a gaggauta ceto mutanen da aka sace a Imo da Borno
NDC ta kuma ce da Dickson ya so, zai iya komawa APC, amma ya zaɓi ci gaba da kasancewa cikin jam’iyyar tare da sauran masu fafutukar ganin an samu sauyin siyasa a ƙasar.
Jam’iyyar ta zargi wasu abokan hamayyarta da yada zargin, tana mai cewa hakan na da alaƙa da ƙara samun karɓuwar NDC a faɗin ƙasar.
Ta kuma yi kira ga magoya bayanta da su yi watsi da zarge-zargen, su ci gaba da gudanar da ayyukan siyasa domin samun nasara ga ɗan takararta na shugaban ƙasa, Peter Obi, da abokin takararsa, Rabiu Musa Kwankwaso, a zaɓen 2027.
Sai dai a cikin sanarwar, jam’iyyar ba ta gabatar da takamaiman hujjojin zargin da take musantawa ko kuma sunayen waɗanda ta ce ke yada zargin ba.