Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, FCT, ta gargadi masu ababen hawa da su guji amfani da motoci ba tare da ingantattun lambobin rajista ba, ko kuma motocin da aka ɓoye ko goge lambobin rajistarsu.

Kwamishinan ’Yan Sandan FCT, CP Ahmed Muhammed Sanusi, ya kuma bayar da umarnin kama tare da gurfanar da duk wanda aka samu yana amfani da irin waɗannan motoci ba bisa ka’ida ba.

Rundunar ta ce musamman yadda ake amfani da motocin SUV da lambobin rajista da ba a iya gani na iya haifar da barazanar tsaro, saboda wasu masu aikata laifuka na amfani da irin waɗannan motoci wajen kauce wa ganowa da bin diddigi bayan aikata laifuka.

Haka kuma, rundunar ta yi gargadi kan amfani da jabun lambobin diflomasiyya ko kuma amfani da lambobin irin waɗannan motoci ba tare da izini ba.

Kwamishinan ya umurci jami’an ’yan sanda a sassan FCT da su ƙara tsaurara matakan tabbatar da bin dokokin rajistar ababen hawa, tare da yin aikin cikin ƙwarewa ba tare da amfani da shi wajen karɓar kuɗin haram ba.

Rundunar ta kuma buƙaci mazauna Abuja da su taimaka wajen tabbatar da tsaro ta hanyar kai rahoton motocin da suke zargi ko wasu abubuwan da ba su dace ba ga ofishin ’yan sanda mafi kusa.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *