Rundunar sojojin Operation Fansan Yamma ta ce dakarunta sun ceto wasu mutane da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a kan hanyar Anka zuwa Gadan Manya, a ƙaramar hukumar Anka ta Jihar Zamfara.

A cewar rundunar, lamarin ya faru ne a lokacin da dakarun Sector 2 ke gudanar da sintiri na yau da kullum, inda suka hango wasu ’yan bindiga dauke da makamai suna kai hari kan wasu mutane biyu da ke tafiya a kan babur.

Rundunar ta ce bayan da sojojin suka samu labarin harin, sun gaggauta zuwa wurin, lamarin da ya tilasta maharan tserewa zuwa cikin daji tare da barin mutanen da suka yi garkuwa da su.

An ce bayan ceto mutanen, jami’an tsaro sun ƙara tsaurara sintiri da sauran ayyukan tabbatar da tsaro a yankin, domin hana ’yan bindiga samun damar zirga-zirga cikin sauƙi da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Rundunar ta kuma ce za ta ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro a yankunan da ake fama da barazanar ’yan bindiga, domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron mazauna yankin.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *