Bendel Insurance ta samu babbar nasara a wasan mako na bakwai na gasar Fimiyar Najeriyar, NPFL, inda ta doke Barau FC da ci 4-1.

Kayode Oke ne ya zama gwarzon ɗan wasa yayin fafatawar, inda ya zura ƙwallaye biyu a minti na 33 da na 78 kafin Suraju Lawal ya ƙara ta uku a minti na 86. Sanan kuma Jonathan James ya zura ta hudu a ragar Barau a minti na 90+4.

Ƙwallon da Barau FC ta samu ya zo ne ta hannun Aliyu Sugau, wanda ya ci bugun fenareti a minti na 82.

Rangers International ma ta samu gagarumar nasara da ci 3-1 a kan Abia Warriors. Godwin Obaje ne ya fara buɗe zura ƙwallo a minti na 37 kafin Chidiebere Nwobodo ya ninka a minti hudu bayan dawowa daga hutun rabin lokaci. Emeka Obioma ya rage wa Abia Warriors kwallo daya daga bugun fenariti a minti na 53, amma Akorode Daniel ya tabbatar da nasarar Rangers inda ya ƙara ƙwallo a ƙarin lokaci.

Enyimba FC ta samu nasara da ci 2-0 a kan Plateau United, da kwallayen Ifeanyi Ihemekwele a minti na 29 da kuma Richard Ezinna a minti na 68.

Rivers United ma ta tsare gidan ta ba tare da an zura mata kwallo ba, inda ta doke Ikorodu City da ci 2-0. Samson Olasupo, shi ya fara ci wa mai masaukin baki kwallo a minti na 19, yayin da Chinemerem Ugwueze ya kara ta biyu kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Kwara United ta farfado daga baya inda ta doke Ranchers Bees da ci 2-1. Jamilu Yusuf ya ci wa Bees kwallo a minti na bakwai, amma Toheeb Gidado ya farke wa Kwara United a minti na 50 kafin Stephen Gideon ya kammala juyin nasarar a minti na 77.

Doma United ta tsira da kyar da ci 1-0 a kan Warri Wolves, inda Joshua Abah ya zura kwallo mai kayatarwa a minti na 81.

Niger Tornadoes ma ta samu nasara da ci 1-0 a kan Kun Khalifat, godiya ga kwallon da Ismaila Sarki ya ci a minti na 82.

Babu abin da ya raba Shooting Stars da Nasarawa United yayin da kungiyoyin biyu suka tashi canjaras wato  0-0.

Inter Lagos da Katsina United sun raba maki a wasan da suka tashi ci 1-1. Nura Abdulbari, shi ya ci wa Katsina United kwallo a minti na 34 kafin Kevwe Iyede ya daidaita wa Inter Lagos bayan minti takwas.

Kano Pillars da Sporting Lagos ma sun tashi kunnen doki 1-1. Abdullahi Musa ya zura wa Kano Pillars kwallo a karin lokacin rabin farko, yayin da Valentine Ugwu ya daidaita wa Sporting Lagos minti uku bayan dawowa daga hutu.

Ga sakamakon wasannin na mako na bakwai:

Bendel Insurance 4-1 Barau FC

Enugu Rangers 3-1 Abia Warriors

Doma United 1-0 Warri Wolves

Niger Tornadoes 1-0 Kun Khalifat

Enyimba FC 2-0 Plateau United

Inter Lagos 1-1 Katsina United

Kwara United 2-1 Ranchers Bees

Rivers United FC 2-0 Ikorodu City

Shooting Stars 0-0 Nasarawa United

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *