Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi kira ga gwamnatin tarayya, da gwamnatin Jihar Imo da hukumomin tsaro da su gaggauta ceto mutanen da aka sace a sassa daban-daban na ƙasar.
Atiku ya bayyana cewa sace mutane 20, ciki har da waɗanda ke shirin shiga aikin NYSC, a Jihar Imo abin takaici ne, yana mai cewa wasu daga cikinsu sun samu kubuta, yayin da wasu ke ci gaba da kasancewa a hannun waɗanda suka yi garkuwa da su.
- Najeriya ta jagoranci tawaga zuwa taron IPU karo na 153 a Tanzania
- Sojoji sun ceto mutanen da aka yi garkuwa da su a Zamfara
Ya kuma nuna damuwa kan ɗalibai sama da 70 da aka sace daga Mussa da Lassa a Jihar Borno, waɗanda ya ce watanni sun shude amma har yanzu suna hannun masu garkuwa da mutane.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa, Atiku ya ce iyalan waɗanda aka sace sun cancanci samun sahihin bayani daga gwamnati, yayin da jama’a ke buƙatar sanin matakan da ake ɗauka domin ganin an dawo da waɗanda aka yi garkuwa da su lafiya.
Ya kuma soki yadda matsalar tsaro ke ci gaba da shafar matasa, yana mai cewa suna fuskantar barazana tun daga makarantar sakandare, zuwa jami’a, har zuwa lokacin da suke tafiya sansanonin NYSC.
Atiku ya ce gwamnati na da babban nauyi na kare rayukan jama’a, tare da yin kira da a ƙara ƙaimi wajen magance satar mutane da sauran matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar.
Sai dai ya kuma bayyana cewa zai ci gaba da ƙoƙarin ganin an gina Najeriya mai tsaro da kuma sauƙin rayuwa, inda matasa za su samu damar ƙirƙira, aiki da kuma samun ci gaba.