Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Peter Obi, ya taya malaman Najeriya da na duniya murnar Ranar Malamai ta Duniya da ake bikin kowace ranar 5 ga Oktoba.

Obi ya ce malamai na daga cikin ginshiƙan ci gaban kowace al’umma, saboda rawar da suke takawa wajen gina tunani, tarbiyya da makomar yara da matasa.

Ya yaba wa malaman Najeriya bisa jajircewa da sadaukarwar da suke yi duk da ƙalubalen tattalin arziki da yanayin aiki, tare da kira ga gwamnati da ta ƙara inganta jin daɗinsu, biyan albashi a kan lokaci da samar musu da ingantattun kayan aiki.

Ya kuma ce Najeriya ba za ta iya magance matsalolin yaran da ba sa zuwa makaranta, rashin aikin yi, talauci da ƙarancin ci gaba ba tare da zuba jari mai ɗorewa a fannin ilimi ba.

Obi ya ce ya kamata ilimi ya samu ƙarin fifiko a tsarin kasafin kuɗi da tsare-tsaren gwamnati, tare da bai wa malamai da kayayyakin more rayuwar makarantu kulawar da ta dace.

Ya gode wa malaman Najeriya bisa ci gaba da gina ƙasar “ɗa guda a lokaci guda”, yana mai cewa kyakkyawar Najeriya za ta samu ne ta hanyar saka jari a cikin jama’a.

 

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *