Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya Ministan Ma’adinai da Ƙarafa, Dele Alake, murnar cika shekaru 70, yana bayyana shi a matsayin amintaccen aboki, ɗan’uwa kuma mai jajircewa wajen hidimar ƙasa.

A cikin saƙon taya murnar, Tinubu ya ce Alake mutum ne mai tsayin daka, gaskiya da rikon amana, tare da nuna cewa a cikin shekaru da dama da suka gabata ya san shi a matsayin mutum mai himma da jajircewa wajen cimma sakamako.

Shugaban ya yaba da gudunmawar Alake a aikin jarida, inda ya ce ya yi amfani da alkalamin sa wajen fallasa matsalolin da suka addabi Najeriya, musamman a lokacin mulkin soja da kuma fafutukar dawo da dimokuraɗiyya.

Tinubu ya kuma tuna lokacin da Alake ya kasance Kwamishinan Yaɗa Labarai da Dabarun Sadarwa na Jihar Legas na tsawon shekaru takwas, yana mai cewa ya taka rawa wajen inganta tsarin sadarwar gwamnati da jama’a.

A matsayinsa na Ministan Ma’adinai da Ƙarafa, Tinubu ya ce aikin Alake na ci gaba da samun karɓuwa a Najeriya da wajen ƙasar, musamman saboda rawar da yake takawa a harkokin ma’adinai da kuma jagorancinsa na Africa Minerals Strategy Group.

Shugaban ya yi masa addu’ar samun ƙarin shekaru cikin koshin lafiya, yana mai cewa ya ci gaba da hidima ga Allah, ƙasa da bil’adama.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *