Daraktar Janar ta Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa, NEMA, Zubaida Umar, ta jajanta wa Rundunar Sojin Sama ta Najeriya da iyalan waɗanda abin ya shafa bayan hatsarin jirgin ATR-42 na rundunar a Igbokoda, Jihar Ondo.
NEMA ta ce Zubaida Umar ta tura Daraktan Bincike da Ceto, Air Commodore Bature Usman, domin jagorantar tawagar fasaha zuwa wurin da hatsarin ya afku, don ƙarfafa ayyukan bincike da ceto da sauran hukumomin da ke aikin a wurin.
- Tinubu ya taya Dele Alake murnar cika shekaru 70
- Babu ɗalibin Gamji College da aka sace — Gwamnatin Sokoto ta musanta rahoton Sahara Reporters
Ta kuma yaba da matakin gaggawar da aka ɗauka wajen fara ayyukan ceto, tare da tabbatar da cewa NEMA za ta ci gaba da samar da dukkan tallafin da ake buƙata wajen gudanar da aikin.
Hatsarin ya rutsa da jirgin ATR-42 da ke kan hanyar Benin zuwa Lagos a ranar Litinin, inda mutane 32, ciki har da fasinjoji 25 da ma’aikatan jirgin bakwai, ke cikinsa.
Zubaida Umar ta yi addu’ar Allah Ya jiƙan waɗanda suka rasa rayukansu, Ya bai wa iyalansu haƙurin jure wannan babban rashi, tare da fatan samun sauƙi ga duk wani da ya samu raunuka.