Allah Ya yi wa Malam Nafiu Baba-Ahmed, mni, Sakataren Janar na Supreme Council for Shariah in Nigeria (SCSN), rasuwa.
Rahotanni sun tabbatar da rasuwarsa a yau Talata, 6 ga Oktoba 2026, inda aka bayyana shi a matsayin masani, lauya, jagoran al’umma kuma mai fafutukar kare muradun Musulmi da tabbatar da adalci a Najeriya.
- Tinubu ya ayyana kwanaki uku na zaman makoki bayan rasuwar jami’an Sojin Sama
- Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana alhininsa kan rasuwar Nafiu Baba-Ahmed
Malam Nafiu Baba-Ahmed ya taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da ayyukan Majalisar Shari’a, musamman a fannonin shari’a, manufofin gwamnati, kare haƙƙoƙin addini da kuma harkokin da suka shafi jin daɗin al’ummar Musulmi.
An sanar da cewa za a gudanar da sallar jana’izarsa a Masallacin Ƙasa da ke Abuja bayan sallar Zuhr ta yau, da yardar Allah.
Muna roƙon Allah Ya gafarta masa kurakuransa, Ya karɓi kyawawan ayyukansa, Ya sanya shi cikin Aljannatul Firdaus, Ya kuma ba iyalansa, abokan aikinsa da daukacin al’ummar Musulmi haƙurin jure wannan babban rashi.
Allahummaghfir lahu warhamhu wa thabbit-hu.