Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya sanya hannu kan Dokar Ƙarin Kasafin Kuɗi ta 2026 da ta tanadi ƙarin Naira biliyan 46.369 ga gwamnatin jihar, yayin da ƙananan hukumomi 27 suka samu ƙarin Naira biliyan 17.109.
Jimillar ƙarin kasafin ta kai Naira biliyan 63.478, wanda gwamnan ya ce zai ƙara wa jihar damar aiwatar da wasu ayyukan ci gaba da inganta ayyukan gwamnati.
- NAF ta fitar da sunayen ma’aikata 25 da hatsarin jirgin sama a Ondo ya rutsa da su
- Za a gudanar da sallar jana’izarsa Nafi’u Baba-Ahmed a Masallacin Ƙasa da ke Abuja.
Gwamna Namadi ya umarci ma’aikatu, hukumomi da ƙananan hukumomi da su yi amfani da kuɗaɗen ne bisa tanadin dokar kasafin, tare da tabbatar da gaskiya, ladabtarwa da samun sakamako mai auna.
Ya kuma yi kira ga Majalisar Dokokin Jihar Jigawa da ta ci gaba da gudanar da aikinta na sa ido, domin tabbatar da cewa ƙarin kuɗaɗen sun koma ayyuka da hidimomin da za su amfani al’ummar jihar.