Gwamnan Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ce jihar ta shafe sama da shekaru uku da rabi ba tare da fuskantar wani rikicin ƙabilanci ko na addini ba.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wani taron tattaunawa kan zaman lafiya tsakanin mabiya addinai da aka gudanar a gidan gwamnatin Kaduna, inda ya jaddada muhimmancin haɗin kai da zaman lafiya wajen samun ci gaba.
Ya ce gwamnatin jihar na kokarin tabbatar da cewa kowa ya samu damar cin gajiyar ayyukan ci gaba ba tare da la’akari da addini, ƙabila ko wurin da yake zaune ba.
- Za a gudanar da sallar jana’izarsa Nafi’u Baba-Ahmed a Masallacin Ƙasa da ke Abuja.
- Jigawa ta ƙara kasafin kuɗi da Naira biliyan 63.4 domin ayyukan ci gaba
Sanata Uba Sani ya kuma ce ana zuba jari a fannonin hanyoyi, kiwon lafiya, ilimi, noma, koyar da sana’o’i da sauran muhimman ababen more rayuwa a ƙananan hukumomi 23 na jihar.
Ya bayyana cewa zaman lafiya mai ɗorewa na bukatar adalci, amincewa da juna da kuma tabbatar wa al’umma cewa gwamnati na yi wa kowa adalci.
Gwamnan ya yaba wa shugabannin addinai da na gargajiya bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen ƙarfafa fahimtar juna da zaman lafiya tsakanin al’ummomin Kaduna.