Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya buƙaci jami’an shari’a na rundunar su ƙara ƙwarewa wajen ba kwamandojin soji shawarwarin shari’a cikin lokaci, musamman yayin da rundunar ke faɗaɗa tsarin rundunoninta da ayyukanta a faɗin ƙasar.
Janar Shaibu ya bayyana hakan ne a ranar Talata 6 ga Oktoba, 2026, yayin buɗe wani taron horaswa na musamman ga jami’an Daraktan Ayyukan Shari’a na Sojoji da aka gudanar a Abuja.
Ya ce faɗaɗa rundunar daga ƙarin rundunoni da jami’ai kaɗai bai isa ba, sai an ƙarfafa tsarin da zai tabbatar da bin doka, haƙƙin ɗan Adam da dokokin jinƙai na ƙasa da ƙasa.
- ’Yan sandan Abuja sun ceto wani yaro da ake zargin ya yi yunkurin sace wa ta yarinya a Kuje
- Kotun daukaka kara ta ajingine hukunci kan karar neman belin El-Rufai
COAS, wanda Babban Daraktan Gudanarwa na Sojoji, Manjo Janar Isa Abdullahi, ya wakilta, ya ce yanayin yaƙi da matsalolin tsaro na zamani na ƙara zama mai rikitarwa, don haka kwamandoji a matakai daban-daban na buƙatar samun shawarwarin shari’a masu inganci da suka dace da yanayin aiki.
Ya ce horon zai taimaka wa jami’an shari’a wajen ba da shawarwari kan kare fararen hula daga illolin yaƙi, kare ma’aikatan lafiya da cibiyoyin lafiya, da kuma fahimtar sabbin fasahohi da suka haɗa da basirar wucin gadi da makaman da ke iya aiki ba tare da jagorancin mutum kai tsaye ba.
Janar Shaibu ya jaddada cewa bin ƙa’idojin larura ta soji, tausayi, bambance fararen hula da mayaƙa, daidaita matakin amfani da ƙarfi da kuma yin taka-tsantsan, na da muhimmanci wajen cimma manufofin soja tare da kare fararen hula da kuma tabbatar da amincewar jama’a.
A nasa jawabin, Mukaddashin Daraktan Ayyukan Shari’a na Sojoji, Kanal Samson Okebukola, ya ce jami’an shari’a na rundunar na taka muhimmiyar rawa wajen haɗa dokokin ƙasa da na ƙasa da ƙa’idojin aikin soja.
Ya bayyana su a matsayin “sojoji masu ilimin shari’a” da ke taimaka wa kwamandoji wajen tabbatar da cewa ayyukan soji sun kasance cikin doka.
Ya ƙara da cewa ƙarfafa ƙwarewar jami’an shari’a zai taimaka wajen inganta yanke shawarar kwamandoji, kare fararen hula da sojoji, da kuma ƙarfafa tsarin shari’ar soja a daidai lokacin da rundunar ke faɗaɗa rundunoni, jami’ai da wuraren gudanar da ayyukanta.
Faɗaɗa rundunar Sojin Najeriya daga rundunoni takwas zuwa 12, tare da shirin ɗaukar ƙarin sojoji 28,000, na daga cikin manyan sauye-sauyen da ake yi a tsarin rundunar.
COAS ya sha jaddada cewa ƙarin yawan jami’ai kaɗai ba zai tabbatar da ingantaccen tsaro ba, matuƙar ba a samu ƙwarewar shugabanci, horo da shirye-shiryen aiki ba.