Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bar Abuja zuwa Addis Ababa, Habasha, domin jagorantar wata tattaunawar ƙasashe biyu da aka shirya domin ƙara inganta tsarin samar da abinci mai gina jiki a Najeriya.
Shettima na halartar taron farko na Nigeria-Ethiopia Nutrition Leadership Exchange Visit ne bisa gayyatar Mataimakin Firaministan Habasha, Temesgen Tiruneh, wanda ke jagorantar tsarin ƙasar na tunkarar matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki ta fannoni daban-daban.
- Kotun daukaka kara ta ajingine hukunci kan karar neman belin El-Rufai
- ’Yan sandan Abuja sun ceto wani yaro da ake zargin ya yi yunkurin sace wa ta yarinya a Kuje
Taron zai bai wa jami’an Najeriya da Habasha damar musayar ƙwarewa kan yadda ake tsara tsarin haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi wajen inganta harkar abinci mai gina jiki.
Wannan shiri ya zo ne a daidai lokacin da Najeriya ke ƙoƙarin ƙarfafa Nutrition 774 Initiative, wanda ke da nufin inganta ayyukan abinci mai gina jiki a dukkan ƙananan hukumomin ƙasar.
A yayin ziyarar, tawagar Najeriya za ta duba wasu shirye-shiryen Habasha da suka haɗa da noma, samar da abinci da ayyukan kula da abinci mai gina jiki a matakin al’umma, domin ganin hanyoyin da za a iya amfani da irin waɗannan ƙwarewa wajen inganta tsarin Najeriya.