Kwamishinan ’yan sandan Jihar Ondo, CP Felix Ohagwu, ya kai ziyara wurin da jirgin Nigerian Air Force NAF 931 ya yi hatsari a Igbokoda, ƙaramar hukumar Ilaje.
Kwamishinan ya ce aikin gano gawawwaki da tarkacen jirgin na ci gaba, yayin da jami’an ’yan sanda da rundunar Marine Police ke bayar da tsaro da tallafi ga sauran hukumomin da ke aikin kwato gawawwakin da tarkacen jirgin.
- Shettima ya jagoranci tawagar Najeriya zuwa Habasha kan harkar abinci mai gina jiki
- Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Nigeria, ya buƙaci a ƙarfafa bin doka a ayyukan sojoji
Ya kuma jajanta wa iyalan waɗanda suka rasu da kuma rundunar Sojin Sama ta Najeriya, tare da yin kira ga jama’a da su guji yaɗa bayanan da ba a tabbatar da su ba.
Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta tabbatar da cewa mutane 25 ne ke cikin jirgin, kuma babu wanda ya tsira daga hatsarin da ya faru a Igbokoda.