Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PRP a zaɓen 2027, Donald Duke, ya ce idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa, zai yi ƙoƙarin rage farashin fetur zuwa kusan N300 kan lita.
Duke ya bayyana hakan ne a wata hira da Channels Television, inda ya ce ya kamata a farashin man da ake tacewa domin amfani a cikin gida bisa kuɗin da ake kashewa wajen samar da shi, maimakon farashin kasuwar duniya.
Ya ce Najeriya za ta iya ware wani kaso na ɗanyen man da take hakowa domin amfanin cikin gida, yayin da sauran man za a sayar a kasuwar duniya.
- Yabon Bala Mohammed ga Tinubu ya haifar da cece-kuce kan takarar Makinde
- Tinubu ya karrama marigayi Ralph Obioha kan gudunmawarsa ga dimokraɗiyya
A cewarsa, hakan zai taimaka wajen rage nauyin tsadar makamashi da ke kan ’yan Najeriya.
Duke ya kuma ce farashin mai mai sauƙi zai taimaka wajen ƙara ƙarfin samarwa da rage matsin tattalin arziki, musamman ga masu ƙaramin ƙarfi.
Sai dai wannan dai alkawari ne na ɗan takarar shugaban ƙasa a shirinsa na neman kujerar shugaban ƙasa a 2027, yayin da ake ci gaba da muhawara kan yadda Najeriya za ta daidaita farashin man fetur, samar da makamashi mai araha da kuma dorewar tattalin arziki.