Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, ya ƙaddamar da ingantaccen tsarin samar da ruwan sha na Matazu, a wani mataki da gwamnatin jihar ta ce zai ƙara inganta samun tsaftataccen ruwa ga mazauna yankin da al’ummomin da ke kewaye.
Gwamna Radda ya ce tsarin ruwan, wanda aka fara kafa shi tun shekarar 1996, an inganta shi domin ƙara samarwa da rarraba ruwan sha.
Ya ce sabon tsarin na da rijiyoyi 17, tare da tankin adana ruwa na ƙasa mai ɗaukar lita 350,000 da wani tanki mai ɗaukar kusan lita 15,000.
- EFCC Kano ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da kafafen yaɗa labarai wajen yaƙi da laifukan kuɗi
- An kama matashi mai shekaru 33 yana rubuta jarabawar ƙarin matsayin mahaifinsa a Abuja
Ya ƙara da cewa an sanya na’urorin amfani da hasken rana wajen samar da wutar da za ta tafiyar da tsarin, domin rage dogaro da wutar lantarki ta yau da kullum da kuma tabbatar da ci gaba da samar da ruwan sha.
Gwamnan ya ce zuba jarin da ya kai biliyoyin naira ya nuna muhimmancin da gwamnatinsa ke bai wa muhimman ayyukan more rayuwa.
Sai dai ya bukaci al’ummar Matazu da shugabanninsu su kare kayan aikin, su yi amfani da su yadda ya kamata, tare da tabbatar da cewa ana kula da su akai-akai.
A nasa jawabin, Kwamishinan Albarkatun Ruwa na jihar, Mannir Ayuba Sullubawa, ya ce aikin na daga cikin shirye-shiryen gwamnatin jihar na gyara da faɗaɗa ayyukan samar da ruwan sha a sassa daban-daban na Katsina.
Ya ce gwamnati ta ware kusan wurare takwas domin aiwatar da ayyukan ruwa.
Shugaban gundumar Matazu, Alhaji Iro Maikano, ya yabawa gwamnatin jihar kan ayyukan raya yankin, tare da roƙon gwamnan da ya duba yiwuwar gina hanyar Gwarjo zuwa Mazoji, wadda ya ce za ta inganta zirga-zirga da tallafa wa harkokin noma da ban ruwa.
Gwamna Radda ya kuma yaba wa al’ummar Matazu bisa goyon bayansu ga ayyukan gwamnati da ƙoƙarinsu wajen inganta tsaro, yana mai cewa zaman lafiya da tsaro su ne ginshiƙan samun ci gaba mai ɗorewa.