Shugaban Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON), Ambasada Ismail Abba Yusuf, ya karɓi Shugaban Hukumar Tsaron Fararen Hula (NSCDC), CG Dr Ahmed Abubakar Audi, a ofishinsa da ke Hajj House, Abuja.
Ziyarar ta mayar da hankali ne kan ƙarfafa haɗin gwiwar hukumomin biyu, musamman wajen tsaron mahajjata, kula da zirga-zirgar jama’a da kuma tabbatar da ingantaccen tsari yayin gudanar da ayyukan Hajji.
- An kama matashi mai shekaru 33 yana rubuta jarabawar ƙarin matsayin mahaifinsa a Abuja
- EFCC Kano ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da kafafen yaɗa labarai wajen yaƙi da laifukan kuɗi
Shugaban NSCDC ya yaba da sauye-sauyen da NAHCON ke aiwatarwa wajen inganta harkokin Hajji, tare da tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da bai wa NAHCON goyon baya da haɗin kai.
Shi ma Ambasada Ismail Abba Yusuf ya gode wa CG Audi kan ziyarar, inda ya jaddada aniyar NAHCON ta ci gaba da ƙarfafa haɗin gwiwar hukumomin biyu domin tabbatar da tsaro, walwala da nasarar ayyukan Hajji na gaba.