An kama wani matashi mai shekaru 33, bisa zargin rubuta jarabawar ƙarin matsayin ma’aikatan Hukumar Kula da Ma’aikatan Babban Birnin Tarayya (FCT Civil Service Commission) a madadin mahaifinsa.

An kama matashin ne a rana ta uku ta jarabawar da ake gudanarwa a harabar Jami’ar National Open University of Nigeria (NOUN) da ke Abuja.

Rahotanni sun ce jami’an tsaro da aka tura wajen tabbatar da tsaron jarabawar ne suka gano shi.

A lokacin da ake yi masa tambayoyi, Matashin ya ce mahaifinsa,, wanda ma’aikaci ne a Hukumar Kashe Gobara ta FCT, ba shi da lafiya, kuma shi ne ya umarce shi da ya zauna ya rubuta jarabawar a madadinsa.

Sai dai an samu saɓani kan shekarun mahaifin, inda Matashin ya ce mahaifinsa yana da tsakanin shekaru 67 zuwa 68, yayin da Mahaifinsa ya bayyana cewa zai cika shekaru 60 a watan Fabrairun 2027.

Ya kuma ce ya kammala makarantar firamare a 1977 da sakandare a 1982.

Bayan yi musu tambayoyi da jami’an DSS, an mika mahaifin da ɗan nasa ga ’yan sanda domin gudanar da ƙarin bincike kan lamarin da kuma matakin da ya dace a ɗauka.

Lamarin ya jawo hankali kan matakan tsaro da tantancewar da ake yi yayin jarabawar ƙarin matsayin ma’aikatan FCT, musamman yadda hukumomi ke ƙoƙarin tabbatar da sahihancin tsarin da kuma hana magudi ko wakilcin wani yayin jarabawa.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *