Fitaccen wakilin ‘yan wasa na Hukumar FIFA, Mohamed Babawo Adamu, wanda aka fi sani da Babawo Lecturer, ya bayyana wasu halaye da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Turai ke buƙata daga ‘yan wasa da kuma dalilan da suka sa ‘yan wasan daga yankin Arewacin Najeriya suka yi ƙaranci idan aka kwatanta da takwarorinsu daga yankin Kudu na ƙasar nan.
Babawo Lecturer ya bayyana hakan ne yayin wani shiri na musamman na neman ‘yan wasa a Kano.
Babawo, wanda ya jagoranci wakilan ƙwallon ƙafa daga Turai da Afirka zuwa birnin Kano a ‘yan kwanaki da suka gabata, ya ce ƙungiyoyi daga ƙasar Spain, da Lithuania da kuma Masar suna neman ‘yan wasan gefe, ‘yan wasan gaba, masu tsaron baya, da kuma ƙwararrun ‘yan wasan tsakiya.
-
Arteta ya sabunta kwantiraginsa da Arsenal har zuwa 2030
-
Cristiano Ronaldo ya bayyana dalilin ficewarsa daga sansanin Portugal
-
Gasar NPFL: Yadda Barau, Plateau da Ikorodu suka sha kaye
“Gaskiya ne. Abun ya matuƙar burgeni da makarantun koyar da ƙwallon ƙafa da na gani a yau, kuma na ga ‘yan wasa hudu ko biyar daban-daban da na san za su iya abun kirki a Turai ba tare da sun dau dogon lokaci ba,” in ji Babawo.
Ya ƙara da cewa masu neman ‘yan wasa sun fi sha’awar musamman ‘yan wasan da za su iya buga salon wasan Turai da sauri.
“Dan wasan da zai tafi Turai ya koyi salon buga wasan su ba tare da daukar dogon lokaci ba, wannan shine abin da muke nufi da na musamman,” in ji shi.
Babawo ya kuma bayyana ƙwarin gwiwa kan hazakar da ’yan wasan yankin arewacin Najeriya ke da su, sai dai ya ce rashin isasshen wayar da kai da kuma rashin hakuri a matsayin babban kalubalen da ke shafar ci gaban wasu matasan ‘yan wasan.
“A ganina, yankin arewacin Najeriya na da hazikan ‘yan wasa,” in ji shi.
“Amma matsalar da muke fuskanta daga wajen wasu ‘yan wasan arewa wani lokaci ita ce wayar da kai. Na biyu, wasu daga cikinsu ba su da hakuri. Za ka ga dan wasa yau a Kungiya A, gobe ka gan shi a wata kungiyar.”
Babawo ya kara da cewa ana kokarin wayar da kan ‘yan wasa, da koca-kocai da masu makarantar koyar da kwallon kafa game da yadda mutum zai gina sana’ar sa ta kwallon kafa da kuma bukatar hakuri yayin neman damammaki a kwallon kafa ta Turai.
Wakilin na FIFA, ya kuma yaba da ingantuwar kayan aikin wasanni a Kano tun ziyararsa ta karshe a 2019, yana mai cewa ci gaban ya zarce hasashensa.
Ya kara da cewa wakilan kungiyoyin kasashen waje da suka ziyarci kasar sun yi matukar burgewa da ingancin kwallon da suka gani.
Babawo, ya yaba wa kungiyar AZuba Football Club da Shugabanta bisa hadin gwiwa a shirin neman ‘yan wasa, yana mai bayyana shirin a matsayin dama ga matasan ‘yan wasa don nuna hazakarsu a gaban kungiyoyin kasa da kasa.
Ya kuma bukaci gwamnati da ta tallafa wa irin wannan shirye-shirye, yana mai cewa shirye-shiryen neman ‘yan wasa na kasa da kasa na iya samar da damammakin aiki ga matasan Najeriya da kuma taimakawa wajen karfafa matasa.
