Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya tabbatar da aniyar gwamnatinsa na ci gaba da tallafa wa ayyukan jinƙai da ci gaban al’umma tare da haɗin gwiwar ƙungiyoyin raya ƙasa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi tawagar Hukumar Kare Fararen Hula da Ayyukan Jinƙai ta Tarayyar Turai, ECHO, wadda jagoran tawagar, Mista Alexandre, ya jagoranta a ziyarar ban girma a Gidan Gwamnatin Jihar Katsina.
Radda ya yaba wa ECHO da ƙungiyoyin da ke aiwatar da shirye-shiryenta kan ayyukan da suke gudanarwa a ƙananan hukumomin jihar, musamman a fannonin abinci mai gina jiki, da samar da abinci da agajin jinƙai ga al’ummomin da ke cikin buƙata.
- Radda zai ƙaddamar da ayyuka da shirin tallafa wa al’umma a Matazu
- NLC ta fara yajin aikin sai abinda hali ya yi a Abuja kan rikicin malamai
Ya ce gwamnatin jihar za ta ci gaba da samar da kuɗaɗe da tallafin hukumomi domin tabbatar da dorewar ayyukan da suka yi nasara, yana mai cewa ya kamata kuɗaɗen gwamnati da tallafin masu bayar da agaji su haɗu wajen samar da ci gaba mai ɗorewa da ya shafi kowa da kowa.
A nasa jawabin, jagoran tawagar ECHO, Mista Alexandre, ya yaba wa Gwamna Radda kan yadda ya sanya buƙatun al’ummomin da ke cikin yanayi na rauni cikin abubuwan da gwamnatinsa ta fi bai wa muhimmanci.
Ya kuma yaba da yadda jihar ke samar da tallafin da ya dace da ayyukan masu bayar da agaji, wanda a wasu lokuta ya zarce adadin kuɗin da masu bayar da tallafin suka tanada.
ECHO ta kuma tabbatar da aniyarta ta ci gaba da tallafa wa Katsina a fannonin abinci mai gina jiki, da samar da abinci, da agajin jinƙai, da ƙarfafa juriyar al’umma da inganta ƙarfin hukumomin jihar.
Ziyarar, wadda Hukumar Kula da Ci Gaban Jihar Katsina (KTDMB) ta shirya, na daga cikin ayyukan ECHO na bibiyar da tantance ayyukan jinƙai da abokan hulɗarta ke aiwatarwa a jihar.