Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya halarci taron Kwamitin Ba da Shawara na Masu Zuba Jari na kamfanoni masu zaman kansu na West Africa Integration and Investment Summit (WAIIS) a Legas.
Sanwo-Olu ya ce taron ya ba mahalarta damar tattauna hanyoyin ƙarfafa kasuwanci tsakanin ƙasashen Yammacin Afirka da kuma jawo ƙarin zuba jari a masana’antun da za su samar da ci gaban tattalin arziki ga yankin.
- EFCC Kano ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da kafafen yaɗa labarai wajen yaƙi da laifukan kuɗi
- Gwamna Radda ya ƙaddamar da ingantaccen tsarin ruwan sha a Matazu
Taron ya samu halartar Shugaban Saliyo, Julius Maada Bio, da ɗan kasuwa Tony Elumelu, yayin da Alhaji Aliko Dangote ya tura wakili.
Sanwo-Olu ya ce Yammacin Afirka na da babbar dama ta bunƙasa tattalin arziki, yana mai cewa ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen yankin zai taimaka wajen mayar da wannan dama zuwa guraben aiki, kasuwanci da ci gaba ga al’umma.
Taron na daga cikin shirye-shiryen WAIIS, wanda ake sa ran gudanar da shi a Saliyo a watan Nuwamba 2026, domin ƙarfafa haɗin kan tattalin arziki, kasuwanci da zuba jari a Yammacin Afirka.