Hukumar Kwastam ta Najeriya, NCS, ta gudanar da shirin wayar da kai kan cutar sankarar mama a hedikwatarta da ke Maitama, Abuja, domin ƙarfafa ilimin jami’ai kan muhimmancin gano cutar da wuri da kuma hanyoyin kariya.
Shirin, mai taken “Inspect, Detect, Protect”, ya haɗa jami’an Kwastam, likitoci da abokan hulɗa, inda aka jaddada muhimmancin duba lafiyar kai akai-akai da neman kulawar likita da zarar an lura da wata alama.
- Gwamna Radda ya ƙaddamar da ingantaccen tsarin ruwan sha a Matazu
- NAHCON da NSCDC sun ƙarfafa haɗin gwiwa kan tsaron mahajjata
Shugabar Ƙungiyar Matan Jami’an Kwastam, COWA, Kikelomo Adeniyi, ta buƙaci musamman mata su riƙa yin gwajin kansu tare da zuwa asibiti da wuri idan sun lura da wani sauyi a jikinsu.
Ta kuma tunatar da maza cewa cutar sankarar mama na iya shafar su.
Hukumar ta ce wayar da kai da gano cutar da wuri na daga cikin muhimman matakan da za su taimaka wajen rage illar cutar.
A yayin shirin, an gudanar da tattaunawar lafiya, bayani daga waɗanda suka tsira daga cutar, zaman tambayoyi da amsoshi, sannan aka yi gwajin sankarar mama kyauta ga jami’ai da sauran mahalarta.