Ƙungiyar matan jami’an ’yan sanda, POWA, reshen Abuja, ta samar da rijiyoyin burtsatse guda biyar domin rage matsalar ƙarancin ruwan sha da ake fuskanta a wasu barikokin ’yan sanda da ke cikin Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Shugabar POWA ta FCT, Hajiya Maimuna Ahmed Sanusi, ce ta jagoranci wannan yunƙuri, inda ta tuntubi Kwamishinan ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, CP Ahmed Muhammed Sanusi, PhD., FCAI, domin samar da rijiyoyin don inganta samun tsaftataccen ruwa ga jami’an ’yan sanda da iyalansu.
- Hukumar Kwastam ta wayar da kan jami’ai kan cutar sankarar mama
- Sanwo-Olu ya halarci taron WAIIS, ya jaddada haɗin kan kasuwancin Yammacin Afirka
Sanarwar da Kakakin Rundunar ’Yan Sandan FCT, SP Josephine Adeh, ta fitar, ta ce samar da rijiyoyin na daga cikin matakan inganta jin daɗin jami’ai da iyalansu, musamman ta hanyar samar da muhimman abubuwan more rayuwa a barikoki.
A cewar sanarwar, Kwamishinan ’Yan Sandan FCT ya yaba wa shugabar POWA ta FCT kan wannan taimako, yana mai cewa inganta jin daɗin jami’ai na da muhimmanci wajen ƙara musu ƙwarin gwiwa da inganta yadda suke gudanar da ayyukansu na kare al’ummar Abuja.