Sakataren yaɗa labarai na kungiyar tuntuɓa ta Arewa (Arewa Consultative Forum – ACF), Farfesa Tukur Muhammed Baba, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta bayyana cikakkiyar gaskiya game da halin da tattalin arzikin ƙasa ke ciki, maimakon rage muhimmancin matsalolin da ‘yan ƙasa ke fuskanta a yau da kullum.

Da yake magana Yayin wata hira da gidan talabijin na Arise News, Farfesa Baba ya jaddada cewa ‘yan Najeriya sun cancanci samun sahihin bayani kan turban da tattalin arzikin ƙasar ke kai domin su samu damar auna kyakkyawan aikin gwamnatin.

“Muna son mu ga wani nau’i na gaskiya,” in ji Baba, yayin da ya buga misali da tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari lokacin da yake neman sake zaɓe inda ya amince da kura-kuransa.

“Ku ba mu sahihin labari mai inganci domin mu yi amfani da shi wajen auna ko za mu iya sake maku ragamar rayuwarmu a hannunku.” in ji shi

Mai magana da yawun na ACF ya jaddada cewa watanni uku sun wadatar ga gwamnati wajen aiwatar da takamaiman matakai na sauƙaƙa tattalin arziki ga al’umma, musamman kudaden makaranta da farashin abinci da ke ƙara hauhawa.

Farfesa Baba ya nuna damuwa mai tsani game da fannin noma, inda ya bayyana cewa ikirarin gwamnati na cewa tattalin arziki yana haɓaka ya ci karo da gaskiyar yadda ake ci gaba da dogaro da shigo da kayan abinci daga waje.

Ya bayyana cewa matsalolin fannin noman ba kawai na rashin tsaro da ‘yan bindiga ba ne, har da tsada mai tsanani na kayan aikin gona.

Yayin da yake fito da tsadar da manoma ke fuskanta, Baba ya ba da misalin yadda manomi ke kashe ₦50,000 wajen gyaran fili da shuka, amma idan ya kai buhu kasuwa sai a saya akan ₦40,000. Ya tsara irin wannan tsarin tattalin arzikin a matsayin “tattalin arzikin tsafi”

A ƙarshe, Farfesa Baba ya buƙaci gwamnati da ta fito fili ta amince inda binciken tasirin manufofinta ya sami kuskure, sannan ta gindaya kudurori masu sauƙi maimakon alkawuran da ba za su yiwu ba.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *