Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Asusun Jama’a, Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo, ya ce yana wakiltar Shugaban Majalisar Dattawa da Majalisar Dattawa ta 10 ta Najeriya a taron ƙasa da ƙasa na EITI na shekarar 2026 da ake gudanarwa a Brussels, Belgium.
Sanata Dankwambo ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na facebook, inda ya ce taron mai taken “Transparency for Shared Prosperity”, wato “Gaskiya da Buɗaɗɗiyar Hanya domin Ci Gaban Jama’a”, ya samar da damar musayar kwarewa da tattauna hanyoyin inganta gaskiya da rikon amana wajen sarrafa albarkatun mai, gas da ma’adinan ƙasa.
- Hukumar Kwastam ta wayar da kan jami’ai kan cutar sankarar mama
- FCT POWA ta samar da rijiyoyin burtsatse biyar a barikin ’yan sanda
Ya ce halartar taron na da nasaba da ƙudurin Majalisar Dattawa na ƙarfafa sa ido kan yadda ake tafiyar da harkokin kuɗaɗen gwamnati da kuma tabbatar da cewa kuɗaɗen da ake samu daga albarkatun ƙasa suna amfani ga ’yan Najeriya.
Sanatan ya ƙara da cewa ’yan Najeriya na da haƙƙin samun cikakken bayani kan kuɗaɗen da gwamnati ke samu, yadda ake amfani da su da kuma sakamakon da ake samu daga kashe su.
Ya ce ingantaccen tsarin gaskiya da rikon amana wajen sarrafa albarkatun ƙasa na da muhimmanci wajen inganta ababen more rayuwa, ilimi, kiwon lafiya da samar da damarmakin tattalin arziki.
Sanata Dankwambo ya ce zai yi amfani da abubuwan da zai koya daga taron wajen ƙara tallafa wa ayyukan sa ido na Majalisar Dattawa da kuma ci gaba da hidima ga al’ummar Najeriya.